Alhamis 28 Mayu 2026 - 18:15
Kada Ku Mayar da Saɓani Marar Tushe —Ko Ma Mai Tushen—Zuwa Rigima da Rarrabuwar Kai 

Hauza/ Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci a cikin wani sako da ya aikawa jama’a a bikin tunawa da ranar buɗe zaman Majalisar Shura ta Musulunci (Majalisar Dokoki) karo na farko, da kuma farkon shekara ta uku ta aiki na Majalisa ta 12, ya jaddada cewa: wajibi ne kowane mai sadaukarwa da zuciyarsa ke bugawa saboda Musulunci da juyin juya hali, ko kuma saboda ‘yancin kai da ɗaukakar Iran, daga yanzu ya ƙara himma wajen kare haɗin kai da dunkulewar al’umma; kada kuma ya mayar da sabani marar tushe —har ma da mai tushen—zuwa rikici da rarrabuwar kai.

A bisa rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an wallafa saƙon Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, a ranar zagayowar ranar buɗe majalisar dokoki ta farko da fara shekara ta uku ta majalisa ta 12.

Ga fassarar cikakken saƙon Ayatullah Sayyid Mujtaba Hussaini Khamenei, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci:

Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai.

Ina taya daukacin al'ummar Iran mai daraja da kuma wakilan majalisar dokoki ta Musulunci murnar bikin Sallah Babba (Id al-Adha) da kuma zagayowar ranar buɗe majalisar dokoki ta farko. A wannan gaba, ina kuma bayyana godiyata ga ƙoƙarin da wakilan majalisar suke yi, musamman mai girma kakakin majalisa, Dr. Qalibaf, wajen ɗaukaka ƙasar.

Majalisar Dokoki ta Musulunci ita ce tsantsar al’umma, alamar dimokuraɗiyyar addini, kuma ginshiƙin doka da tsarin kafa doka a Jamhuriyar Musulunci, wadda take da muhimmiyar rawa wajen aiwatar da nufin jama’a. Yanzu, bayan watanni uku da suka wuce tun daga 'Kariya Mai Tsarki ta Uku', an tabbatar wa abokai da maƙiya hakikanin ƙimar cikin rai da asalin halayen jama’ar Iran a cikin imani, fata, da aiki; kuma ɗaukakar matsayin jama’ar Iran ta nuna wani haske mai ban mamaki na tsantsar falalolin al’umma a fili.

Tunda yake wakilin gaskiya na al’umma dole ne ya kasance daga cikin jinsin al’umma, wannan lokaci na yanzu wata muhimmiyar gabar bayyanar kishin al’umma ce a cikin wakilai da Majalisar Dokoki ta Musulunci, domin su daidaita rawar da za su taka da gudanar da nauyin da ke kansu daidai da matsayin al’ummar da aka tayar; sannan da aiki da ƙoƙari ninki biyu, su gaggauta da zurfafa ayyukan kafa doka da sa ido a kan hanyar shimfiɗa makomar Iran ta Musulunci.

A wannan fagen jihadi, kujerar wakilci tana matsayin sansanin layin gaba na sauyi a tafarkin ci gaban ƙasa. Saboda haka, ya dace wakilan al’umma, tare da dogaro da taimakon Allah Maɗaukaki da neman ceton jagoranmu kuma shugabanmu (Imamul Mahdi - AS), da kuma kiyaye mutuncin jinin shahidai masu daraja na yaƙe-yaƙe biyu da Amurka da Sahiyoniya suka ƙaƙaba mana, waɗanda babban jagoranmu shahidi (Allah ya ɗaukaka matsayinsa) yake kan gaba, su yi aikin jihadi da dukkan ƙarfinsu domin gudanar da mulki tare da gwamnati da sauran hukumomi, tare da kiyaye ƴancin ikon majalisa, a kan tafarkin gina ƙasa yadda ya dace, magance damuwar jama'a—musamman matsalolin tattalin arziki da na yau da kullum, bunƙasa masana'antu da ayyukan yi, ɗaukaka matsayin ilimi da sana'o'i, bunƙasa al'ada da ɗabi'u, yaƙi da cin hanci da rashawa, shawo kan hauhawar farashi da tsadar rayuwa, da kuma kawar da talauci ta kowane fanni. 

Saboda haka, ya zama wajibi dokoki da ƙudurorin da Majalisa ke amincewa da su su kasance suna da alaƙa kai tsaye kuma a bayyane da manyan matsalolin ƙasa da bukatun jama’a, kuma su kasance masu nufin haifar da fata da gina makomar ƙasa. Al’umma, kafin komai, tana bukatar ganin alamomi na ainihin fata, hanya mai ɗorewa kuma tabbatacciya, da hangen nesa mai haske game da gaba, domin ta iya tsara rayuwarta da motsi bisa wannan tushe. Wakilan Majalisa kuma, ta hanyar matsayinsu, kudurorinsu da jawabansu, za su iya mayar da Majalisar Dokoki ta Musulunci wata cibiya mai jagorar samar da fata; daga ciki har da cewa a wannan halin da ake ciki, tare da haɗin gwiwar bangaren zartarwa da na shari’a, su mayar da hankali kan taken “Tattalin Arziki Mai Juriya (Economy of Resistance), a ƙarƙashin haɗin kan ƙasa da tsaron ƙasa” a shekarar 1405 (2026), su sanya a matsayin manyan ajandar aiki: tabbatar da daidaiton tattalin arziki, rage hauhawar farashi, sarrafa yawan kuɗi a kasuwa (liquidity), bunƙasa samarwa, gyara Shirin Ci gaba na Bakwai, da kuma ƙara batutuwan da suka shafi sabunta ƙasa da sake gina asarar da yaƙe-yaƙen tilas na biyu da na uku suka haifar; sannan su zana taswirar hanyar tafiyar gwamnati da sauran sassa a yanayin da ake ciki da kuma a zamanin bayan yaƙi.

Domin aiwatar da rawa da ta dace da matsayin “al’ummar da aka tayar”, ana buƙatar wasu shiri da sharudda daban-daban. A cikin wannan taƙaitaccen lokaci, ina ba ‘yan’uwa maza da mata shawarar su yi nazari mai zurfi da gaske kan cikakkun bayanan maganganun babban jagora shahidi mai girma (Allah Ya ɗaukaka matsayinsa), a ganawar sa ta duk shekara da wakilan Majalisar Dokokin Musulunci—musamman a shekarun baya-bayan nan—saboda suna ɗauke da darajar kwarewa da umarnin aiwatarwa mai muhimmanci. A bayyane yake cewa kiyaye taƙawa ta mutum tana da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da bin waɗannan shawarwari da kuma sauke manyan ayyuka yadda ya kamata a wannan lokaci mai matuƙar muhimmanci. Haka kuma: gane abubuwan da suka fi fifiko daidai, yanke hukunci bisa bincike, yin zurfin shawarwari na ƙwararru, rayuwa tare da jama’a da faɗaɗa hulɗa da su, yaƙi da cin hanci da rashawa ta kowane fanni, fifita moriyar ƙasa da buƙatun jama’a a kan bukatu da moriyar bangaranci, ƙungiyanci ko na yanki, kula da diflomasiyyar majalisa, jarumtaka da bayyana matsayi a sarari da ƙarfi a gaban kwaɗayin masu girman kai, da kuma lura da hankali da ruhin juyin juya hali ga sabon matsayin Iran a yankin da duniya—duk waɗannan na daga cikin sharuddan da ake bukata. Daga cikin misalan taƙawa kuma akwai kiyaye babbar ni’imar haɗin kan ƙasa da wannan dunkulewar da ba ta da misali wadda aka bai wa al’ummar da aka tayar a ƙarƙashin tutar Iran ta Musulunci, kuma tana daga cikin muhimman dalilan samun nasara a gaban “Babban Shaiɗani”.

Godiya ga wannan ni’ima ita ce: kowane ɗan ƙasa, musamman masu tunani da siyasa—ciki har da wakilan Majalisa—su yi ƙoƙari wajen kare wannan haɗin kai, su nisanci saɓanin siyasa marasa amfani, kuma kada su ƙara haskaka banbance-banbancen zamantakewa. Makircin abokin gaba makaho—bayan yaƙin tilas, matsin tattalin arziki, da killacewar farfaganda da siyasa—shi ne haifar da rarrabuwar kai da tarwatsa al’umma domin ya rama shan kayen da ya sha a fagen soja kuma ya durƙusar da al’umma. Saboda haka, ya zama wajibi kowane mai sadaukarwa wanda zuciyarsa ke bugawa domin Musulunci da juyin juya hali, ko kuma domin ‘yancin kai da ɗaukakar Iran, daga yanzu ya ƙara ƙoƙari fiye da da wajen wajen kare haɗin kan sahun al’umma mai dunkulewa da juna; kada ya mayar da saɓanin da ba shi da tushe, har ma da wanda yake da tushen, zuwa rikici da rarrabuwar kai; kuma su kasance—ta magana da ta aiki—abin koyi na haɗin kai da dunkulewar al’umma, in sha Allah.

Ina yi muku fatan samun nasara a wannan nauyi mai matuƙar girma na wakiltar al’umma ta gari wadda ta tsaya ƙyam a gaban zalunci da farmakin mugaye da ɓatattu na wannan zamani, tana kuma jagorantar tarihi zuwa tafarki madaidaici. Da fatan addu’ar shugabanmu (Allah Ya gaggauta bayyanarsa mai tsarki) ta zama mai taimako, mai daidaita matakai, kuma mai jawo muku dacewar Allah.

Wassalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuh

Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei

7 ga Khordad, 1405 (28 ga Mayu, 2025)

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha